Hausa translation of the meaning Page No 354

Quran in Hausa Language - Page no 354 354

Suratul Al-Nur from 32 to 36


32. Kuma ku aurar da gwaurãye daga gare ku, da sãlihai daga bãyinku, da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadãtar da su daga falalarSa. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani.
33. Kuma waɗannan da ba su sãmi aure ba su kãme kansu har Allah Ya wadãtar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke nẽman fansa daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansã idan kun san akwai wani alhẽri a cikinsu kuma ku bã su wani abu daga dũkiyar Allah wannan da Ya bã ku. Kuma kada ku tĩlasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu, ( 1 ) dõmin ku nẽmi rãyuwar dũniya, kuma wanda ya tĩlasta su to, lalle Allah, a bãyan tĩlasta su, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
34. Kuma lalle ne Mun saukar zuwa gare ku, ãyõyi mãsu bayyanãwa, da misãli daga waɗanda suka shige daga gabãninku, da wa'azi ga mãsu taƙawa.
35. Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misãlin HaskenSa, kamar tãgã, a cikinta akwai fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi taurãro ne mai tsananin haske, anã kunna shi daga wata itãciya mai albarka, ta zaitũni, bã bagabashiya ba kuma bã bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma kõ wuta ba ta shãfe shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa. Kuma Allah na buga misãlai ga mutãne, kuma Allah game da dukan kõme, Masani ne.
36. A cikin waɗansu gidãje waɗanda Allah Yã yi umurnin a ɗaukaka kuma a ambaci sũnansa a cikinsu, sunã yin tasbĩhi a gare Shi a cikinsu, sãfe da maraice.
( 1 ) Tsaron kai, shi ne su yi aure; tĩlastãwa a nan, shi ne a hana su aure dõmin su yi wa ubangijinsu aiki.